Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Abubakar ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima a Sokoto cewa ba za a yi amfani da dokokin Shari’ar Musulunci ga waɗanda ba Musulmai ba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Sultan Sa’ad ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a fadarsa, a lokacin da masu kula da harkokin ƴan bautar kasa karkashin jagorancin shugabansu suka kai masa ziyarar ban girma.
Ya kuma tabbatar musu cewa, za su samu tsaro duk da cewa, akwai kalubale na tsaro a kasar baki daya.
Abubakar ya kara cewa za a kyale su su gudanar da addinansu.
Ya bayyana cewa ba za a dora wa wadanda ba Musulmi ba hukuncin Shari’ar Musulunci, kuma ya jaddada cewa babu wanda za a tursasa wa shiga Musulunci ba da son ransa ba.
“A Sakkwato, Shari’ar Musulunci ta sauka ne kawai a kan Musulmai, babu wanda zai tursasa masa saka hijabi, ko bin Shari’ar Musulunci idan ba Musulmi ba ne,” ya bayyana


