Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce, har gobe shi ne shugaban jam’iyyar APC duk da hukuncin da alƙalin babbar kotun jihar Kano ya zartar na cewa ya daina bayyana kansa a matsayin mamba a jam’iyyar.
Tsohon gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje ya ce sun rubuta takardar koke kan alƙalin da ya tabbatar da dakatarwar da aka yi masa tare da sanar da jami’an tsaron ƙasar cewa wanda ya bayar da sanarwar dakatar da shi cewa sojan gona ne.
Ya shaida wa BBC cewa “abubuwan da suke faruwa abubuwa ne waɗanda dole sai mun tashi sosai da sosai domin sabon shaƙiyanci ne yake nema ya shiga dimokraɗiyya a Najeriya musamman a jihar Kano.”
Ga tattaunawar da wakilinmu Khalifa Shehu Dokaji ya yi da tsohon gwamnan Kano, Ganduje.