Shugaban kungiyar Shakhtar Donetsk Rinat Akhmetov, ya yi alkawarin tallafa wa ƴakin Ukraine da £22m bayan sayar da Mykhailo Mudryk zuwa Chelsea.
Chelsea ta sayi ɗan wasan ne a ranar Lahadi kan kuɗi £89m, wadda shi ne irinsa na farko da aka sayi ɗan wasa daga Ukraine.
Akhmetov ya ce kuɗin zai taimaka wa wani shiri na koƙarin mazauna Mariupol da kuma iyalan sojoji da aka kashe.
“Ina son na gode wa dukkan mutane a faɗin duniya da suka taimaka wa Ukraine,” a cewar Akhmetov.
“Muna iya magana a kan kwallon kafa a Ukraine a yau saboda taimakon sojojin ƙasar da mutanenta da kuma goyon bayan illahirin duniya.” in ji Akhmetov.
Rasha ta mamaye Ukraine ne a watan Febrairun 2022.