fidelitybank

Shafukan sada zumunta ya kamata su buɗe ofisoshin su a Najeriya – Ɗan Majalisa

Date:

Dan majalisar da ke wakiltar yankin Delta ta Arewa Sanata Ned Nwoko, ya buƙaci shafukan sada zumunta daban-daban da ake amfani da su a kasa su kafa ofishin su.

Nwoko ya yi wannan kiran ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce an shirya kiran ne saboda wasu dalilai da suka hada da samar da kudaden shiga, saukin kasuwanci, saukin korafe-korafe da kararraki, samar da ayyukan yi da dai sauransu.

Sanatan ya ce kasancewar manyan kafafen sada zumunta na zamani a kasar nan na da matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, magance rikice-rikice, da samar da kudaden shiga ga al’umma.

A cewarsa, Najeriya, kasa mafi yawan jama’a a Afirka da ke da mutane sama da miliyan 200, tana yin cudanya da shahararrun shafukan sada zumunta.

“Wadannan dandamali na sada zumunta na kasa da kasa da ake amfani da su a Najeriya sun hada da Facebook, X, Instagram, WhatsApp, YouTube, Snapchat, da TikTok.

“’Yan Najeriya sun zo na daya a Afirka saboda yawan amfani da kafafen sada zumunta da kuma na biyu a duniya, inda a kullum suke amfani da intanet na tsawon sa’o’i uku da mintuna 46, a cewar sabuwar kafar yanar gizo ta Global Web Index (GWI) kamar yadda Business Insider Africa ta ruwaito.

“Duk da yawan amfani da wadannan kafafen sada zumunta da ‘yan Najeriya ke yi a kasar, har yanzu wadannan kamfanoni ba su kafa ofisoshi a Najeriya ba,” in ji Nwoko.

Ya ce akwai nasarorin da aka samu na wasu kamfanoni na kasa da kasa, irin su MTN Group, Shell, Chevron, Nestle, Total, P&G, da dai sauransu, wadanda suka kafa ayyuka a Najeriya, wanda ya taimaka matuka wajen bunkasar tattalin arzikin kasa da ci gaban fasaha.

“Duk da haka, babban abin da ba ya nan shi ne kasancewarsu a Najeriya, al’ummar da ke matsayi na biyu a duniya a fannin amfani da Intanet da kafofin sada zumunta,” in ji Nwoko.

legitnews.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp