Kamfanin Twitter ya gaya wa ma’aikatansa cewa zai rufe dukkanin ofisoshinsa tun daga yanzu har zuwa ranar Litinin.
Sai dai a sakon da ya aika musu bai bayyana dalilin rufewar ba.
Ana dai ganin daruruwan ma’aikatan kamfanin da ya shiga wani hali na ajiye aikinsu da shi ko kuma suna shirin yin hakan.
Tun bayan da ya saye shi a kan dala miliyan dubu hudu sabon mai kamfanin Elon Musk ya sallami kusan rabin gaba dayan ma’aikatansa, manya da kanana.
Haka kuma ya bai wa sauran wadanda suke nan wa’adin su sanya hannu a yarjejeniyar aiki tukuru na karin sa’o’i ko kuma su san inda dare ya yi musu.