fidelitybank

Shafi Mulera: Ku daina ɗaukar doka a hannu – Jami’an Tsaro

Date:

Rundunar ƴan sandan Babban birnin tarayya, ta gargaɗi mazauna yankin kan ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da aikata laifuka, domin gudun tayar da zauna tsaye.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun jami’arta ta yaɗa labaru da hulɗa da jama’a, SP Josephine Adeh, ta ce ta yi gargaɗin ne bayan yunƙurin da wasu mutane suka yi na hukunta wani mutum da aka zarga da satar al’aura a yankin Karshi na babban birnin tarayyar.

Sanarwar ta ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda wasu maza uku suka ce sun ji wani yanayi da ba su gane ba a al’aurarsu bayan haɗa jiki da mutumin.

Bayan hakan ne dandazon mutane suka far wa wanda ake zargin, sai dai jami’an ƴan sanda sun ceci shi sa’ar da suka isa wurin, jim kaɗan bayan bayan fara ɗaukar matakin.

Dalilin haka ne kwamishinan ƴan sanda na yankin birnin tarayyar, CP Haruna G. Garba ya buƙaci jama’a da su guji ɗaukar irin wannan mataki.

A cikin kwanakin nan an riƙa yaɗa labaru, waɗanda ba a tantance ba kan ɓullar mutane masu satar al’aura bayan haɗa jiki ko kuma shan hannu da al’umma.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp