Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar ADP, kuma dan majalisar wakilai, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya yi Allah-wadai da haramta amfani da babura a manyan tituna.
Sha’aban wanda ya soki dokar hana baburan masu ƙafa uku kan manyan titunan jihar da gwamnatin jihar ta yi ya yi gargadin cewa matakin ya saba wa ka’idojin ci gaban bil’adama.
Sha’aban Ibrahim Sharada ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin majalisar yakin neman zabensa, Abbas Yushau Yusuf ya raba wa manema labarai a Kano.
Ya ce, a daidai lokacin da ya kamata gwamnati ta bullo da dabaru, domin magance tashe-tashen hankulan matasa tare da karkatar da hankalinsu daga aikata laifuka da shaye-shayen miyagun kwayoyi, maimakon haka ta mayar da hankali kan hana zirga-zirgar.