Tsohon dan wasan Manchester City, Sergio Aguero, ya bayyana cewa yana dab da komawa fagen kwallon kafa a matsayinsa na mai kungiya.
Sai dai Aguero ya ki bayyana sunan kungiyar.
Dan wasan mai shekaru 36 ya fadi hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da dan wasan Argentina, Coscu, ainihin suna Martin Perez Disalvo.
Da aka tambaye shi ko yana son komawa kwallon kafa a matsayin koci, tsohon dan wasan Barcelona ya ce: “Gaskiyar magana ita ce ina tunanin shiga kungiyar kwallon kafa a matsayin mai shi.
“Ba zan ce ko wane kulob ne ba, amma ina ganin muna kan hanya madaidaiciya.
“Ina son in sami damar gudanarwa, don taimakawa kulob din ya ci gaba, don gina kungiya mai kyau, ma’aikata masu kyau.”
Aguero ya yi ritaya daga buga kwallon kafa a shekarar 2021 bayan da aka gano cewa yana fama da bugun zuciya da ba a saba ba kwanaki bayan an kai shi asibiti.