fidelitybank

SERAP ta maka Tinubu a kotu

Date:

Ƙungiyar kare hakkin ƴan ƙasa da tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya ‘SERAP’ ta kai ƙarar shugaba Bola Tinubu kotu kan gazawar sa wajen hana tsofaffin gwamnonin da suke rike da mukamin minista karbar kudaden fansho na jihohi.

Kungiyar SERAP dai na neman kotu ta tilasta wa Tinubu ya umarci wadannan tsofaffin gwamnonin da su daina karbar irin wadannan kudade.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi, mataimakin shugaban ƙungiyar a Najeriya, Kolawole Oluwadare, ya ce ministocin da abin ya shafa su ne Nyesom Wike da Bello Matawalle da Adegboyega Oyetola.

Sauran tsofaffin gwamnonin sun hada da Badaru Abubakar da David Umahi da Simon Lalong da Atiku Bagudu da kuma Ibrahim Geidam.

Sanarwar ta ce ““Nadin waɗanda ke karbar fansho na rayuwa a matsayin ministoci wani aiki ne na son rai da kuma saɓa wa ƙa’ida”.

“Yayin da da yawa daga cikin ‘yan waɗanda suka ajiye aiki ba a biyan su kuɗaɗen fansho ba, tsofaffin gwamnonin da ke rike da mukamin minista na samun makudan kuɗaɗen alawus-alawus idan sun bar ofis.”

“Gwamnatin Tinubu tana da nauyin hana tsofaffin gwamnonin karbar duk wani hakki na ritaya yayin da suke aiki a matsayin ministoci.”

SERAP dai ta ce wannan dabi’a ba ta dace ba, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.

Amma kuma har yanzu ba a sanya ranar sauraron karar ba.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp