fidelitybank

SERAP ta maka Akpabio da Tajudeen a gaban kotu

Date:

A yayin da ake ta cece-kuce, kungiyar kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa (SERAP), ta shigar da karar shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, kan kin kawo karshen ayyukan da ba bisa ka’ida ba na kayyade alawus-alawus na ‘yan majalisa da kudin tafiyar da su.

Kolawole Oluwadare, Mataimakin Daraktan SERAP ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

A cewar SERAP, an shigar da karar ne a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja mai lamba FHC/ABJ/CS/1289/2024.

SERAP ta ce, “Odar mandamus na umurtar da tilasta Mista Akpabio da Mista Abbas su bayyana ainihin adadin kudaden gudanar da ayyukan da ‘yan majalisar ke biya da kuma karban duk wata, da kuma bayanan kashe kudaden gudanar da ayyukan,” in ji SERAP.

Kungiyar ta kara da cewa “Tattalin da sakin layi na N, sashe na 32 (d) na Jadawali na Uku ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 [kamar yadda aka gyara] ya haramtawa Majalisar Dokoki ta kasa gyara ma’aikata albashi, alawus-alawus da kudaden tafiyar da ayyukanta.”

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa ‘yan majalisa na gyara albashi da alawus-alawus dinsu, sabanin shawarar hukumar tattara kudaden shiga (RMAFC).

Ko da yake an fayyace cewa Sanatoci 109 a Najeriya suna karbar albashin N1,063,860 duk wata, amma bai bayyana adadin alawus-alawus din ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sanatan Kano ta Kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce Sanatoci na samun Naira miliyan 21 a duk wata.

Shehu Sani, wanda tsohon Sanata ne, ya ce ikirarin Sumaila kan kudin gudanar da aiki ya tabbatar da shi.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp