Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta kai ƙarar gwamnonin jihohin ƙasar 36 da ministan birnin tarayya Abuja, saboda zarginsu da gaza yin bayanin yadda suka kashe maƙudan kuɗaɗen da suka samu daga kason Asusun Tarayya na FAAC, tun daga shekarar 1999.
Cikin wata sanarwar manema labarai da mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare ya fitar ranar Lahadi, ya ce ƙungiyar ta ɗauki matakin ne sakamakon rahoton da ta samu cewa a cikin watan Maris FAAC ta raba naira tiriliyan 1.123 tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi.
Haka kuma sun raba naira tiriliyan 1.208 a watan Aprilu, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.
SERAP ta ce FAAC ya raba wa jihohin ƙasar 36 naira biliyan 398.689 a watan Maris kawai, yayin da aka raba musu naira biliyan 403.403 a watan Afrilu.
Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci kotun ta tilasta wa gwamnonin tare da ministan Abuja, su gayyato hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasar, watau EFCC ta ICPC domin su binciki zarge-zargen almundahana da kason arzikin da jihohin ke samu daga asusun tarayyar, tare da yin nazarin yadda jihohin suka kashe kuɗaɗen.
Ƙungiyar ta ce ”Yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda gwamnonin jihohin ke kashe kuɗaɗen jihohinsu ciki har da kason da suke samu daga asusun tarayya”.
SERAP ta kuma koka kan yadda ta ce ”duk da ƙarin kuɗin da jihohin suka samu daga FAAC ɗin, har yanzu miliyoyin al’ummominsu na fama matsanancin talauci da rashin muhimman abubuwan more rayuwa.
Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa ”sakamakon cire tallafin man fetur da ƙoƙarin gwamnatin tarayya na farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, gwamnatin ƙasar ta ƙara wa jihohin abin da suke samu daga FAAC, amma duk da haka babu wani cigaba da aka samu a fannin tsaro da walwalar miliyoyin ‘yan ƙasar”.
SERAP ta yi zargin cewa jihohin ƙasar 36 da Abuja na kashe kuɗaɗen da suke samun daga asusun FAAC ta hanyoyin da ba su dace ba.
“Muna zargin cewa kuɗaɗen da suke samu daga FAAC, suna amfani da su ne ta hanyoyin da ba su dace ba tare da karkatar da su zuwa wasu fannoni, ga kuma batun yin watsi da ayyukan da suka fara. Haka kuma muna zargin jihohin da kashe kuɗin kan wasu abubuwa kamar yaƙin neman zaɓe da sabgogin siyasarsu”, in ji sanarwar.