Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya ce, ƙasar sa za ta yi amfani da ribar da za ta samu daga cinikin man fetur da aka fara tonowa wajen gina ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan da ƙasar da ke yammacin Afirka ta fara tono man fetur karon farko a tarihi.
Fitaccen kamfanin makamashi na Australian ”Woodside” ya bayyana tono man a matsayin ranar tarihi, kuma wani abun ci gaba ga kamfanin da kuma Senegal.
Shirin tono man da aka yi wa laƙabi da Sangamor, wanda ya haɗa da iskar gas, na da niyyar tono gangar man fetur 100,000 a kowace rana.
Ana sa ran shirin zai samar wa Senegal biliyoyin daloli, tare da bunƙasa tattalin arzikinta.
Babban manajan kamfanin man fetur na ƙasar, Thierno Ly, ya ce ƙasar ta buɗe sabon babi, a lokacin da aka ƙaddamar da tono man ranar Talata.
Shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye, wanda aka zaɓa a watan Afrilu ya jima yana burin ƙulla yarjejeniyar fara aikin, a wani ɓangare na sauye-sauyen da ya alƙawarta samar wa ƙasar a lokacin yaƙin neman zaɓe.