Ƙasar Senegal ta bi jerin ƙasashen da ke da arziƙin man fetur a Afirka ta yamma, wani abun da ya nuna cewa tattalin arziƙin ƙasar na bunƙasa.
A makon da ya wuce ne ƙasar ta fara haƙo man a karon farko bisa tsammanin samar da ganga 100,000 a kowace rana.
Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya tabbatar wa da kasar cewa Senegal za ta amfana daga kuɗaden sayar da man da iskar gas kuma za a alkilta su.
“Mun kafa wata gidauniya wadda jikokin-jikokinmu za su amfana.” In ji shugaba Faye.