Nasarar da Senegal ta samu na nufin shi ne karo na uku da masu rike da kofin nahiyar Afirka ke kaiwa matakin zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya.
Duka lokuttan da suka gabata Najeriya ta kai matakin 16 na karshe a shekarar 1994 da 2014.
Wannan sakamakon kuma shine karo na farko da Senegal ta yi nasara sau biyu a jere na kai bantanta wasan gaba.
Sun kai matakin gaba ne a karo na biyu, bayan sun kai matakin daf da na kusa da karshe a karon farko a shekara ta 2002.
A halin da ake ciki kuma Cody Gakpo dan kasar Holland ya sake zura kwallo a ragar Netherlands a matsayi na daya a rukunin A, wanda hakan ya kawo karshen Qatar a gidanta na gasar cin kofin duniya da rashin nasara na uku a jere.