Ministan babban birnin tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya caccaki wasu shugabannin jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas, bisa bayyana goyon bayansu ga gwamna mai ci, Siminalayi Fubara.
Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja.
Rahotanni na cewa, jiga-jigan jamâiyyar PDP a jihar Ribas, Abiye Sekibo; tsohon shugaban PDP na kasa, Uche Secondus; Tsohon dan takarar gwamna, Celestine Omehia; da tsohon dan majalisa, Austin Opara; A makon da ya gabata ne suka ayyana goyon bayan Fubara tare da yin kira ga shugaban kasar da ya gargadi Wike.
Sai dai da yake mayar da martani a ranar Talata, Wike ya ce Sekibo, Secondus, Omehia da Opara duk âyan siyasa ne da ba su cancanci a kira su da âdattawan jihohi baâ.
Ministan babban birnin tarayya Abuja ya ce duk ba su da wani tasiri yayin da ya kore su daga jamâiyyar.
Wike ya dage kan cewa Secondus ba dan jamâiyyar PDP ba ne saboda dakatarwar da aka yi masa a kotu.