Kocin Everton Sean Dyche, ya mayar da martani kan rahotannin Alex Iwobi zai bar Toffees a bazara.
An alakanta Iwobi sosai da komawa Fulham da kasa da kwana daya a karshen kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bazara.
Lokacin da aka tambaye shi game da ci gaba da cece-ku-ce game da makomar dan wasan na Najeriya, Dyche ya ba da takaitacciyar amsa ga Liverpool Echo yana mai cewa, “Amo ne a halin yanzu.”
Iwobi dai ya rage shekara daya a kwantiraginsa a Goodison Park, kuma tattaunawa kan tsawaita wa’adin ya ragu.
Dan wasan mai shekaru 27, babban dan wasa ne a kungiyar ta Merseysiders, kuma magoya bayansu za su yi bakin cikin ganin ya bar kungiyar.
An nada ƙwararren ɗan wasan tsakiya a matsayin gwarzon ɗan wasan Everton a kakar wasa ta ƙarshe.


