Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA), ta umurci kulob din kasar Masar, Smouha SC da ya biya dan wasan gaba na Najeriya, Junior Ajayi dala 70,000.
Ajayi ya kai rahoton Smouha ga hukumar kwallon kafa ta duniya bayan kungiyar ta yi watsi da shi.
Dan wasan gaba ya samu rauni yayin wasan sada zumunci da kungiyar Canal Club a watan Oktoban 2022.
Dan wasan mai shekaru 27 ya yi ikirarin cewa kulob din ya bar shi ba tare da kula da shi ba kuma ana bin sa bashin albashi.
FIFA ta baiwa Smouha wa’adin kwanaki 15 ya biya Ajayi dala 70,000.
Ya koma kungiyar ne a watan Oktoban da ya gabata bayan ya yanke hulda da kungiyar Al-Nasr Benghazi ta Libya.