fidelitybank

Sauyin Yanayi: Kasashen Yamma munafukai ne – Buhari

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nuna yatsa ga ƙasashen Yamma ya na mai kiran su da ‘munafukai” saboda gazawarsu wajen ɗaukar matakan da suka dace kan sauyin yanayi.

“Da yawa daga cikin takwarorina [shugabannin ƙasa] na nuna damuwa game da munafurcin ƙasashen Yamma da gazawarsu wajen kasa ɗaukar matakin da ya dace,” a cewar shugaban cikin wata maƙala da ya rubuta wa jaridar Washington Post ta Amurka.

Shugaban ya jaddada cewa shugabannin Turai sun sha nuna gazawa wajen cika alƙawarin samar da dala biliyan 100 don shawo kan “matsalar sauyin yanayi da suka haifar da kansu” ga ƙasashe masu tasowa.

Ya ƙara da cewa daga yanzu ba zai yiwu ƙasashen Turai su dinga tsara yadda ya kamata ƙasashen Afirka za su yi amfani da ma’adanan da suke da su ba.

“Kar ku faɗa wa ‘yan Afirka yadda ya kamata su yi amfani da arzikinsu. Da a ce Afirka za ta yi amfani da dukkan arzikin iskar gas da take da shi a rumbuna, wanda shi ne mafi inganci ga muhalli, hayaƙin da ke gurɓata yanayin duniya zai tashi daga kashi 3 cikin 100 zuwa 3.5.”

Afirka na fitar da kashi kusan uku ne kacal na hayaƙi mai gurɓata muhalli a duniya baki ɗaya amma tana cikin nahiyoyin da suka fi kowace fuskantar bala’in sauyin yanayin.

daily post today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp