Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress, AAC, Omoyele Sowore a ranar Laraba, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, kan sabbin takardun kudi na naira da aka yi wa kwaskwarima.
Sowore ya zargi Buhari da Emefiele da wasa da ‘yan Najeriya ta hanyar sake fasalin Naira.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, dan takarar shugaban kasa na AAC ya bayyana shugaban kasar da gwamnan CBN a matsayin ‘yan damfara.
Ya kuma jaddada cewa babu wani gagarumin sauyi da ya samu kan Naira, kuma da alama an sake yaudarar ‘yan Najeriya.
Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da kuma N1000 a yayin fara taron mako na majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Sabbin takardun Naira za su fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Disamba, yayin da tsofaffin za su daina aiki daga ranar 1 ga Fabrairu, 2023.
Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 19 da Najeriya za ta sake fasalin wasu takardun kudinta.
Da yake raba hoto a shafin Twitter, Sowore ya nuna rashin jin dadinsa game da ci gaban.
Ya rubuta: “@GodwinIemefiele na bankin @cenbank, kuma @MBuhari dai ya yi wa ‘yan Najeriya wasa kan zamba da ake kira sake fasalin Naira. Babu wani abu da aka “sake fasalin” kawai canjin rini. ‘Yan damfara! #Bazamu Cigaba Kamar Wannan ba.”


