Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga a fadar gwamnatin Jihar Oyo a ranar Talata, suna nuna rashin amincewa da matakin gwamna Seyi Makinde na sauya sunan makarantar zuwa Omololu Olunloyo Polytechnic, Ibadan.
Ɗaliban, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar ɗalibai (SUG), Olamide Oladipupo, sun ce sunan da makarantar take da shi yana da tarihi da martaba, don haka ya kamata a bar shi yadda yake kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Makinde ya sanar da sauya sunan kwalejin ne a ranar 26 ga Yuni, 2025 yayin jana’izar tsohon gwamnan jihar, Dr. Omololu Olunloyo, wanda shi ne shugaban farko na makarantar kuma ya taɓa zama gwamnan jihar a shekarar 1983.
Sauya sunayen manyan makarantu a Najeriya yana ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, inda ɗalibai da tsofaffin ɗalibai ke bukatar a soke irin wannan mataki.