Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade a ranar Juma’a, 25 ga Maris, 2022, zai san makomarsa, biyo bayan karar da jam’iyyar PDP ta shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja na ficewa daga jam’iyar.
Jam’iyyar ta shigar da kara ne inda take neman a ba da umarnin korar Ayade da mataimakinsa, Ivara Ejemot Esu kan sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da dai sauransu.
PDP ta bakin lauyanta, Emmanuel Ukala, SAN, ta shigar da karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/975/2021 a gaban mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja.
Daily Independent ta rawaito cewa, kotun 7, inda mai shari’a Taiwo, zai saurari karar da PDP ta shigar ranar Juma’a 25 ga watan Maris.
Idan dai za a iya tunawa, Taiwo, a ranar Litinin din da ta gabata, ya umarci ‘yan majalisar wakilai biyu da ke wakiltar Cross River da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar 18 da su bar kujerunsu saboda sauya sheka zuwa APC.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne biyo bayan karar mai lamba FHC/ABJ/CS/971/2021 da PDP ta shigar a ranar 27 ga Agusta, 2021 domin kalubalantar sauya shekar ‘yan majalisa 20 zuwa APC, tare da gwamnan a ranar 20 ga Mayu, 2021.