fidelitybank

Sauya jam’iyya: Ranar 11 ga watan Afiliru Yakubu Dogara zai san makomar sa

Date:

A ranar 11 ga watan Afrilu ne dai aka sanya ranar shari’ar da ake yi na neman korar tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara kan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PDP da shugabanta na jihar Bauchi Hamza Akuyam ne suka shigar da karar a gaban mai shari’a Donatus Okorowo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a shekarar 2020.

Dogara ya wakilci mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro na jihar Bauchi a majalisar wakilai.

Jam’iyyun da ke cikin karar sun hada da Shugaban Majalisar Wakilai, Babban Lauyan Tarayya (AGF), Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kuma Jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa tsohon shugaban majalisar, a karkashin sashe na 68 (1) (g) na kundin tsarin mulkin kasar, bai cancanci zama majalisar wakilai ba bayan ya yi watsi da jam’iyyar PDP, wadda a kan dandalin ta ya ci zaben sa a 2019.

Kimanin makonni biyu da suka gabata mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya kori gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da mataimakinsa Kelechi Igwe da kuma wasu ‘yan majalisar dokokin jihar su 15 da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, mai shari’a Taiwo Taiwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ya kori ‘yan majalisar dokokin jihar Cross River su 20 saboda sauya sheka daga PDP zuwa APC.

legitnewsnigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp