Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC, ta ce, yau saura kwana 100 a buɗe rumfunan zaɓe a fadin ƙasar
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Tuwita, mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar Farfesa Mahmod Yakubu, ya ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, sannan mako biyu baya a yi na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa ba gudu ba ja da baya game da amfani da na’urar tattara sakamakon zaɓe da tantance masu kada ƙuri’a a lokacin babban zaɓen da ke tafe.