Sabon dan wasan Liverpool, Cody Gakpo, ya bayyana cewa ya kusa shiga kungiyoyin Premier Manchester United da Leeds United kafin ya koma Anfield.
A kwanakin baya ne Gakpo ya koma Liverpool daga PSG Eindhoven a kan kudi kusan fam miliyan 35.
Da yake magana da Mirror, dan wasan na Netherlands ya ce, “Abu ne mai wahala a wannan bazarar. Lokaci ne mai tsanani sosai.
“Na yi tunanin zan tafi Manchester United, amma a ƙarshe, abin bai yi nasara ba. Leeds United ta shigo.
“Su kulob ne mai kyau, amma na tambayi kaina ko da gaske zan je wurin kuma lokacin da kuke shakka, ba shi da kyau.”