fidelitybank

Saura kiris a kammal kasuwar Gwal a Kano – Ministan Ma’adanai

Date:

Ministan ma’adinai da karafa, Olamilekan Adegbite, ya tabbatar da cewa, za a kammala aikin kasuwar Zinariya wato Gwal a jihar Kano kafin karshen shekarar 2022.

Ministan y a bayyana haka ne a ranar Talata a Kano a lokacin da yake duba aikin ginin katafaren kasuwar ta zinare.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai taken gwamnatin tarayya domin kammala Kano Gold Souk a bana da ma’aikatar ta fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnatin Buhari ta ba da tabbacin cewa, za ta kammala aikin kasuwar Gwal a Kano kafin karshen shekarar 2022.”

Ya ci gaba da cewa, “Samar da kasuwar a Kano na daga cikin kokarin gwamnati mai ci na samar da dabarun kere-kere na fasaha da kananan ma’adanai a kowane shiyyoyi shida na siyasar kasar nan, domin yin amfani da damar masu sana’a da masu hakar ma’adinai. masu aiki a kasar.”

Ministan ya na cewa, “Muna so a kara habaka gwal dinmu a Najeriya, domin mu kara daraja, mu samar da ayyukan yi ga jama’armu tare da samar da kudaden shiga ga gwamnati,” in ji shi.

An gina katafaren kasuwar ta Zinare ne a karamar hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano, kuma a na ci gaba da aikin na tsawon watanni hudu.

vanguard new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp