Masu fafutuka a Saudiyya sun ce an yankewa wasu mutane uku ‘yan kabilar al Huweitat da ke da karfin fada a ji hukuncin kisa.
Masu fafutukar sun ce mutanen uku wanda suka hada da kani da dan uwa da kuma sirikin Abdul Rahim al Huwaiti ne wanda ya rasu a yayin wani musayar wuta da jami’an tsaro a 2020, bayan yaki ya bayar da kadararsa a yi amfani da ita wajen gudanar da wani aiki.
Kabilar Huweitat, ta yadu a sassan arewa maso yammacin Saudiyya da Jordan da kuma Masar.