fidelitybank

Saudiyya ta yanke hukuncin kisa ga ƴan ta’adda huɗu

Date:

Rahotanni daga Saudiyya na bayyana cewa hukumomi sun zartas da hukuncin kisa kan wasu ƴan ƙasar guda huɗu a cikin kwanaki biyu da suka gabata, bayan samun su da laifukan ta’addanci.

Hakan ya kawo waɗanda aka zartaswa hukuncin kisa a ƙasar zuwa mutum bakwai a wannan watan, waɗanda yawanci suka fito daga yankunan da ƴan Shi’a suka fi rinjaye.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ta ruwaito ma’aikatar harkokin cikin gida na cewa cikin laifukan da aka samu mutanen, sun haɗa da leƙen asiri da kafa kungiyoyin ta’addanci da far wa jami’an tsaro da kuma koyon sarrafa maƙamai da amfani da bama-bamai.

Hukumomin Saudiyya sun zartas da hukuncin kisa kan mutum 36 tun soma wannan shekara, idan aka kwatanta da 147 na bara, a cewar bayanai da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun sha sukar masarautar ta Saudiyya kan ƙaruwar mutanen da take zartas wa hukuncin kisa

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...
X whatsapp