Firaministan Birtaniya Rishi Sunak da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman sun amince a zaman da suka yi cewa rasa rayukan mutane da ba su ji ba ba su gani ba a Zirin Gaza da Isra’ila a cikin makonni biyu da suka gabata yana da ban tsoro, a cewar kakakin Firaministan.
Sunak, wanda ya isa Riyadh tun da farko, ya karfafa wa Saudiyya gwiwa da ta yi amfani da tasirinta don “tallafawa zaman lafiya” a Gabas ta Tsakiya, a cewar sanarwar da kakakin Firaministan ya fitar.
Sunak da bin Salman “sun jaddada wajibcin Æ™aucewa fantsamar yaÆ™in” da kuma É—aukar matakan da suka dace don cimma wannan buri.
Sanarwar ta ƙara da cewa firaministan da Yarima mai jiran gado sun amince da buƙatar kai agajin a Gaza domin samar da ruwa da abinci da kuma magunguna.


