Saudiyya ta ce ta samu nasarar karbar bakuncin wasannin hunturu na yankin Asiya na 2029.
Za a gudanar da wasannin ne a wani katafaren wajen shaƙatawa da ke kan tsuani wanda ba za a kammala gina shi ba sai shekarar 2026.
Ministan wasanni na ƙasar Yarima Abdulaziz BinTurki Al-Faisal ya ce shirin Trojena zai samar da “wani yanayi na hunturu a cikin sahara.”
Za a samar da wasannin tseren ƙanƙara da na ruwa. Wajen shaƙatawar yana daga cikin shirin ƙsar na kashe dala biliyan 500 na shirin Neom – wani katafaren yanki da za a gina mai cike da fasaha a kusa da Kogin Maliya.