Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Saudiyya, ta kammala shirya jiragen da za su yi jigilar mahajjata daga Minna zuwa Dutsen Arafat a shirye-shiyen Aikin Hajjin bana.
Hukumar dai ta kwashe tsawon watanni tana kula tare da gwajin jiragen, domin tabbatar da lafiya da ingancinsu, don samun damar jigilar mahajjatan zuwa muhimman wuraren da za su ziyarta a yayin aikin hajjin.
Jiragen wadanda aka sanya wa suna Haramain za su taimaka wa Mahajjatan isa muhimman wuraren cikin hanzari da kwanciyar hankali.