Ƴan sanda a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, sun kama wasu ƴan ƙasar biyu, sakamakon dukan da suka yi wa wani ma’aikaci a wani rukunin shaguna a birnin.
A wani bidiyo da ya rinƙa yawo a shafukan sada zumunta, an gansu suna ta dukan ma’aikacin.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa wata sanarwa da jami’an tsaron suka fitar ta ce bayan binciken wucin gadi da aka yi, an gano cewa lamarin ya faru ne sakamakon rashin jituwar da aka samu a wurin biyan kuɗi a shagon.
Rahotanni sun ce, ana ɗaukar matakan shari’a a kansu domin ganin an hukunta su