Shugaban Manyan masallatai biyu mafiya tsarki a duniya, Masallacin Makkah da kuma na Madina, Sheikh Sudais, ya kaddamar da wata manhaja ta maraba da maniyyata a cikin harsuna, wadda aka yi mata lakabi da Turancin Ingilishi “In your languages, we welcome you.”
Tsari ne da za a rika yi wa maniyyata a Masallatan Harami da Shabbakin Manzon Allah (SAW) bayani da kuma yi musu jagora cikin harsuna 23 na duniya.
Maniyata daga kasashen duniya na cigaba da sauka a kasar Saudiyya, domin gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2022.