Wata kungiyar kare ‘yancin dan’adam a Saudiyya, ta ce, an yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara 16 a gidan yari saboda ya sake tura wani sako a shafin tiwita.
Kungiyar masu kare hakkin dan’adam ‘yan Saudiyya a nahiyar Turai da ke da sansani a Jamus ta ce wata kotu ta musamman ce ta yanke wa Nasr a-Mubarak hukuncin a kasar Saudiyya.
Sai dai kungiyar kare hakkin dan’adam din ba ta yi karin haske a kan abin da sakon tiwitar ya kunsa ba.
Hukuncin ya yi daidai da salon matakin hukumomin Saudiyya na daure ‘yan kasar tsawon lokaci saboda kawai sun furta albarkacin bakinsu a kan shafukan sada zumunta.
Wani lamari a baya-bayan nan da ya faru a kan Salma al-Shehab ya ja hankalin al’ummar duniya inda aka yi ta yin tur lokacin da aka yanke wa dalibar da ke karatu a Jami’ar Leeds hukuncin dauri na shekara 34 saboda tana bin shafi da sake tura sakonnin ‘yan fafutuka da masu nuna bijirewa ga gwamnatin Saudiyya.