fidelitybank

Saudiyya ta dakatar da duk wani mai niyar shiga kasar ta sai masu aikin Hajji kawai

Date:

Ƙasar Saudiyya ta ce daga ranar 29 ga watan Afrilun da muke ciki ba wanda za ta bari ya shiga ƙasar sai mai ɗauke da bizar aikin hajji.

Jaridar Saudi Gazzet ta ambato ma’aikatar cikin gida ta ƙasar na bayyana haka cikin sabbin matakan da ta ɗauka kan tsare-tsaren aikin hajjin bana.

Sabbin matakan sun tanadi cewa za a haramta wa ƴan asalin ƙasar mazauna ƙetare shiga birnin Makka, in ba da wani muhimmin dalili ba.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa za a bai wa asalin ƴan ƙasar izinin shiga birnin Makka ne kawai idan adireshin gidansu ya nuna cewa a birnin suke da zama, ko waɗanda aka bai wa damar yin aiki a harami.

A cewar ma’aikatar harkokin cikin gidan wannan wani mataki ne manyan sauye-sauye da ta ɓullo da su domin lura da aikin hajjin bana na tabbatar da lafiya da tsaron mahajjata.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa daga ranar 13 ga watan Afrilu, ƙasar za ta daina bayar da biza ga masu zuwa ibadar Umara, yayin da ta saka ranar 29 ga watan Afrilun a matsayin ranar da masu ziyarar Umara daga ƙasashen waje za su fice daga ƙasar, domin bayar da damar shirye-shiryen aikin hajji.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp