Hukumomin Saudiyya sun ɗauki mataki na magance yaɗuwar ruwan ZamZam na jabu a ƙasashen duniya.
Shafin Twitter na hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya sun wallafa hotunan robobin ruwan ZamZam na gaskiya domin ankarar da al’umma.
“Sakamakon rahotannin da ake samu na gurɓataccen ruwan ZamZam a sassa daban-daban na duniya da suka haɗa da Birtaniya da Afirka da kuma Australia.
“Waɗannan su ne hotunan robobin ruwan ZamZam na gaskiya ba na jabu ba,” a cewar sanarwar.