Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa bana za a gudanar da itiƙafi a Masallatan Harami lokacin azumin watan Ramadan.
Shafin Haramain Sharifain ya rawaito cewa nan gaba kadan ne za a fitar da tsarin gudanar da itiƙafi a shafin intanet na hukumar da ke kula da masallatan biyu.
Wanna ne karon farko da za a gudanar da itiƙafi cikin shekaru biyu tun bayan bullar cutar korona. In ji BBC.