fidelitybank

Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa ga mutane 81

Date:

Saudiyya ta sanar da cewa ta ƙaddamar da hukuncin kisa a kan mutum 81 da kotu ta yanke wa hukunci kan laifuka da suka shafi ta’addanci da fyaɗe da kisa, kamar yadda kamfanin labarai na ƙasar SPA ya ruwaito.

Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce daga cikin mutanen akwai mambobin ƙungiyar ISIS da Al-Qaeda da Houthi.

“Mutanen da suka kai 81, an yanke musu hukunci ne kan laifuka daban-daban, ciki har da kashe mutane maza da mata da yara ƙanana,” in ji sanawar.

“Laifukan sun haɗa da shiga ƙungiyoyin ta’adddanci na ƙasashen waje kamar ISIS da Al-Qaeda da Huothi da ke kai hare-hare a cikin ƙasa (Saudiyya) da kuma zuwa wuraren rikici don taya ƙungiyoyin ta’addanci yaƙi.”

Ta ƙara da cewa an kama mutanen ne sannan aka yi musu shari’a a Saudiyya ƙarƙashin jagorancin alƙalai 13 a mataki uku daban-daban na shari’a kan kowane ɗayansu. In ji BBC.

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp