fidelitybank

Saudiyya ta ƙwace naman Kajin da suka lalace na tan sama da biyar

Date:

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Saudiyya (SFDA), ta ƙwace tan biyar na naman kajin da ya lallace a wani gidan ajiye kayyakin abinci da ke birnin Riyadh.

Hukumar ta tabbatar da cewa gidan ajiyar kayan abincin ya saɓa wa ƙa’idoji masu yaw, cikin har da yin ƙarya sayar da kayayyakin da suka lalace, inda ake sake wa naman kajin mazubi tare da sanya musu sabbin kwanan watan lalacewa.

Haka kuma hukumar ta ce gidan ajiyar ya saɓa wa dokokin lafiya, da amfani da ma’aikatan da ba su da takardun shaidar karatun lafiya.

SFDA ta kuma rufe gidan ajiyar tare da lalata duk kayyakin da ta ƙwace.

Hukumar ta ce ta gudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwwar hukumar gudanarwar birnin Riyadh da ma’aikatar kasuwanci da ma’aikatar walwala da ci gaba jama’a da hukumar zakka da haraji ta ƙasar tare kuma da hukumar fasa ƙwauri ta ƙasar.

Haka kuma hukumar ta yi kira ga kwastomomi da su kai rahoton duk wani shago ko kamfanin da ya sayar musu da kayayyakin da suka lalace. In ji BBC.

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp