Jiragenn ruwa maƙare da kayan agaji daga ƙasashen Saudiyya da Kuwait da Italiya ya isa tashar ruwan birnin Derna na Libya.
Jiragen dai shake suke da Tantuna, da barguna da kayan abinci, da ruwan sha mai tsafta. In ji BBC.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ma ta ce tuni magungunan da ta aika suka isa birnin, da ambaliyar ruwa ya ɗaiɗaita a makon da ya wuce.
Inda madatsun ruwa da dama suka ɓalle.
Sama da mutum 12,000 suka mutu a mummunar ambaliyar ɗauke da ruwan sama da guguwa, yayin da kawo yanzu ba a san inda sama da mutum 10,000 suke ba.


