Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya c,e barazanar satar mai na da babbar barazana ga yankin Neja Delta.
Gwamna Diri, wanda ya ba da tabbacin hadin kan jihar don magance satar man fetur, ya yi kira da a dauki matakan gaggawa don kawo karshen mummunan halin da ake ciki a yankin da kuma kasa baki daya.
Da yake jawabi a gidan gwamnati, Yenagoa, a ranar Litinin, lokacin da ya karbi tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, Gwamna Diri ya bayyana cewa satar mai ya yi matukar illa ga muhalli da kimar yankin.
Gwamna Diri, ya koka da yadda satar man fetur da ke shafar gwamnati a dukkan matakai, ya hana al’ummar yankin abin da za su yi amfani da su, yana mai jaddada cewa idan ba a daina ko kuma a rage shi sosai ba, lamarin zai yi tsanani.