Sarkin Sudan na Wurno, Ambasada Shehu Othman Malami ya rasu.
Marigayin ya rasu ne a Masar bayan ya sha fama da jinya.
An haifi marigayin a Sokoto a shekarar 1937.
Ya rike mukamai ciki har da jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu a lokacin marigayi Janar Sani Abacha.
Sannan ya kasance shugaban hukumar gudanarwar bankuna da dama a Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana rasuwar basaraken na Sokoto a matsayin babban rashi ba ga iyalansa ba kadai har da gwamnatin Najeriya da kuma daukacin al’ummar jihar Sokoto.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma ‘yan uwan marigayin.