Sarkin Tikau da ke jihar Yobe Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn-Grema ya rasu.
Dan uwan Sarkin Alhaji Abubakar Talba ne ya tabbatar da rasuwar yayan nasa, yayin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na NAN da ke Damaturu a ranar Asabar.
Tamba wanda shi ne Yariman Tikau, ya ce ibn-Grema ya mutu ne a Potiskum ranar Juma’a da misalin karfe 4 na yamma.
“Eh zan iya tabbatar muku da cewa Sarkin ya mutu bayan wata gajeriyar jinya da ya yi. Ya mutu yana da shekara 70,” in ji shi.
Yariman ya ce za a rufe gawar sarkin mai daraja ta daya ne a yau Asabar da misalin karfe 4 na yamma, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.