Osolo na Isolo a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka, ya rasu.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da shugaban karamar hukumar Isolo, Olasoju Adebayo ya fitar.
A cewar sanarwar, za a yi jana’izar Sarkin da karfe 4:00 na yammacin ranar Laraba kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sanarwar ta ce: “Ina da umarnin Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, da ya ba da sanarwar rasuwar babban sarkin masarautar Isolo, Oba Kabiru Agbabiaka, Adeola Olushi III, a yau 10 ga Afrilu, 2024. Ya kasance 64.
“Za a yi jana’izarsa a yau da karfe 4 na yamma a fadarsa, 3/5 Akinbaye Street, Isolo, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Allah ya jikansa ya huta.