Mai martaba Sarkin Kotorkoshi, Ahmad Umar da ke Jihar Zamfara, ya rasu a yau Alhamis.
Sarkin ya rasu yana da shekara 89 da haihuwa.
Ya hau kan karaga a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 1961.
Bayanai sun nuna cewa, sarkin ya rasu a gidansa bayan ya sha fama da jinya.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce, an yi jana’izarsa a yau da Æ™arfe 6:30 a fadarsa da ke Kotorkoshi ta Ƙaramar Hukumar Bungudu.
A watan Maris na 2021 ne aka yi bikin cikar mai martabar shekara 60 a kan karagar mulki. In ji BBC.