Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shawarci zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya kafa ma’aikatar harkokin addini, domin inganta tattaunawa tsakanin addinai da kuma zaman lafiya a kasar nan.
Ya yi wannan kiran ne a wajen bukin kaddamar da Jagoran Facilitators Interfaith, wanda Action Aid Nigeria ta shirya a ranar Juma’a.
Sarkin wanda Hakimin Nasarawa, Babba Dan-Agundi ya wakilta, ya ce, ma’aikatar za ta taimaka wajen inganta juriya da fahimtar addini a tsakanin ‘yan Nijeriya.
A cewarsa “zaman lafiya wani bangare ne na halittu a doron kasa, kuma akwai bukatar a kiyaye ta.”
Tun da farko, Daraktan kungiyar Action Aid Nigeria na kasa, Ene Obi ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su kiyaye nagarta ta tattaunawa tsakanin addinai domin inganta zaman lafiya a kasar.
“Dole ne a gan mu mu zauna lafiya da juna ba tare da la’akari da kabila, addini, da bambance-bambancen siyasa ba don ci gaban siyasar mu baki daya,” in ji shi.