Sarki Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci Sallar Idi a gidan sarki na Nasarawa duk dai a birnin na Kano.
Bayan Idar da sallar ne sarkin na 15, ya hau dokinsa, sannan ya koma gidan sarki da ke nasarawa tare da rakiyar dimbin magoya bayansa.
A cikin makon da ya gabata ne dai rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta haramta hawan sallah a faÉ—in jihar bisa wasu dalilai da tace na tsaro ne.
To sai dai gwamnatin jihar ta ‘yan sandan ba su tuntuÉ“eta ba a lokacin da suka fitar da sanarwar.