Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Jama’are, Alhaji Dakta Ahmadu Muhammad Wabi na III rasuwa.
Ya rasu ne da misalin Æ™arfe 12 na daren Asabar, wayewar garin Lahadi kamar yadda Gado Da Masun Jama’are, Alhaji Saleh Malle ya tabbatar wa BBC.
Sarkin dai ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Ya dai shafe kimanin shekara 50 a kan karagar mulki, kuma ya bar mata biyu da ‘ya’ya 35, da kuma jikoki da dama.
Ana sa ran yin jana’izarsa idan anjima a garin na Jama’are.