Sarkin Birtaniya Charles III ya wallafa saƙo tare da hoton da ya fi so na Sarauniya Elizabeth II domin tunawa da cikar mahaifiyar tasa shekara guda da rasuwa.
Cikin saƙon, Sarki Charles lll ya ce yana tunawa da irin “jajircewar da ta nuna wajen hidimta wa ƙasar”.
Hoton da sarkin ya zaɓa ya nuna sarauniyar a lokacin da take matashiya mai shekara 42, da aka ɗauka a shekarar 1968.
Ranar 8 ga watan Satumban 2022 ne Sarauniya Elizabeth II ta rasu a fadarta da ke Balmoral tana da shekara 96 a duniya.
Mutuwar tata na zuwa ne watanni bayan bikin cikarta shekara 70 a kan gadon sarauta.
A saƙon alhinin da ya aike, Sarki Charles lll ya gode wa ƙasarsa kan “ƙauna da goyon baya” da suka nuna masa shi sa matarsa sarauniya Camilla a tsawon shekararsa guda ta farko da ya yi a kan gadon sarauta.
“A yayin da ake cika shekara guda da rasuwar mai martaba sarauniya, da kuma hawanmu karagar mulki, muna iya tuna irin sadaukarwar da ta yi wajen hidimta wa ƙasarmu,” in ji sarkin.
“Haka kuma ina matuƙar godiya bisa soyayya da goyon baya da kuka nuna mini ni da matata a shekararmu ta farko a kan kadon sarauta, a yayin da muke iya bakin ƙokarinmu wajen hidimta muku”


