Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya auri wata budurwa ‘yar shekara 22, A’isha Yahuza Gona.
Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa, daurin auren da aka yi a garin Safana na Jihar Katsina.
Majiyar ta ce, Sarkin ya daura auren ne a wani biki na kasa da kasa bayan wata ‘yar gajeriyar zawarcin da ta shafe mako guda kacal.
Amaryar diya ce ga Alhaji Yahuza Gona, tsohon shugaban karamar hukumar Safana.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, amaryar ta riga ta shiga sabon gidanta tare da mijinta a Daura.
Rahotanni sun bayyana cewa, Sarkin ya auri wata amarya ‘yar shekara 20 mai suna Aisha Iro Maikano a watan Disambar bara.