Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce, idan sarki ya kammala sallar juma’a, zai koma masaukinsa da ke gidan gwamnatin jihar inda hakimai za su ci gaba da kai gaisuwa ga sarki.
Tuni manyan hakimai da sauran manyan masu riƙe da sarauta a masarautar Kano sun yi mubaya’a ga Sarki Muhammadu Sanusi II.
Cikin jawabin sanar da naɗin sarkin da gwmanan jihar ya gabatar ranar Alhamis, ya ce ya bai wa duka sarakunan da aka rushe wa’adin sa’o’i 48 da su kwashe kayansu su fice daga fadojinsu, domin bai wa sabon sarki damar shiga fadar.